Wani Neman Jarumai . Морган Райс
Чтение книги онлайн.
Читать онлайн книгу Wani Neman Jarumai - Морган Райс страница 14
Amma bayan lokaci mai kama da har abadan, mayakin ya mayar cewa: “Ka bi mashigi na gabas, sai ka mike arewa iya iyawanka. Sai ka shiga mashigi na uku a gefen hagu, sanan inda hanya ya rabu ka bi dama, a wani rabuwan kuma kabi dama. Ka shige ta lankwashashen saman mashigi na dutse, sai kaga wurin horonsu a gaba da mashigin. Amma ina mai gayamaka, kana bata lokacinka. Basu yin maraba da maziyarci.
Abinda Thor ya bukaci ji kenan kawai. Batareda jiran wani bugun zuciyarsa ba kuma, ya juya ya wuce filin a guje, yana bin kwatancen, yana maimaitasu a cikin kwakwalwarsa, yana kokarin tuna su. Ya ga rana ya haura sosai a sama, sai yafara adu’an kawai lokacida shi zai kai, kar ya zama ya makara.
*
Thor ya gangara tsabtatattun, hanyoyi da jeren kaura a dan guje, yana murduwa da juyawa a kan hanyansa na tafiya a cikin fadan sarki. Yayi iya kokarinsa na ganin yabi kwatancen, yana fatan ba batar dashi a ke yi ba. Daga can karshen harabar, yaga dukkanin mashigun, sai ya zabi na uku a gefen hagu. Ya shigeshi a guje sai yabi wurarenda hanyan ya rabu kamar yada a ka gaya masa, yana juyawa hanya bayan hanya. Yayi gudu yana fuskantan masu zuwa, dubban mutane masu kwararowa cikin birnin, taron nata karuwa a kowane minti. Ya goga kafadu da masu hura algaita, masu carafke, masu shaila da ire iren masu nishadantar da mutane, kowanne ya ci ado na musamman.
Thor ya gagara hakuri da tunanin a fara zabe batare dashiba, sai yanata kokarin ya tara hankalinsa a yayinda yake juyawa hanya bayan hanya, yana neman wani alama na filin horon. Ya wuce a karkashin wani lankwashashen saman mashigi, ya juya wata hanyar, sai ga, can da nisa, ya hangi abinda kawai zai iya zama inda ya nufa ne: dan karamin haraba, a gine da duwatsu a kewaye dai dai. Mayaka na tsaron katon mashigi dake sakiyarsa. Thor yaji dan ihu daga bayan katangunsa sai bugun zuciyarsa ya karu. Nan ne wurin.
Ya fita a guje, huhunsa a bude. Yayinda yakai mashigin, mayaka biyu sun matso gaba suka sauke su mashinsu, suka tare hanya dasu. Wani mayaki na uku ya maso gaba ya daga hanu daya.
“Saya a wurin,” ya bada umrni.
Thor ya daskare, yana numfashi sama sama, Kaman zai gagara boye murnarsa.
“Ba…zaka…ganeba,” ya sauke numfashi, kalmomi na fadowa daga bakinsa a sakanin numfashi, “Dole na kasance a ciki. Na makara.”
“Makara ma me?”
“Zaben.”
Mayakin, wani gajeren, mutum mai nauyi da zazzana a fata, ya juya ya kalli shauran, suma suna mayar da kallon rashin yarda. Ya juya ya kalli Thor daga sama zuwa kasa da wani kallon rashin yarda shima.
“An shigar da sabobin daukan tun sa’o’in da suka wuce, a safaran sarauta. Idan ba a gayyace ka ba, ba za ka shiga ba.”
“Amma ba ka ganeba. Dole ne na---”
Mayakin ya mika hanu ya kama gaban rigan Thor.
Kaine baka geneba, kai yaro mara kunya. Kai waye da zaka zo nan ka nemi shiga ko ta halin kaka? Yanzu katafi----kafin na saka a turu.
Ya ture Thor, wanda ya fada baya da taku dayawa.
Thor yaji Kaman harbi a cikin kirjinsa a inda hanun mayakin ya tabashi--- amma fiye da haka, yaji harbin an kishi. Yaji wannan rashin adalci ne. Bai iso har nan kawai domin wani mayaki yazo ya mayar dashi batare da ma anganshi bane. Ya daura zuciyan saishi ya shiga.
Mayakin ya juya zuwaga mutanensa, shi kuma Thor ya tafi, ya juya dama ya kewaya kewayayen ginin. Yana da wata shiri. Ya cigaba da tafiya har ya bace, sai ya fara dan gudu, yana bin jikin dangan. Ya duba domin ya tabbattar mayakan basu kallonsa, sai ya kara gudu sosai, daya kai rabin hanyan kewayan ginin ya hangi wata mashigin haraban---a can sama akwai lankwasassun budi a dutsen, a kare da sadunan karfe. Daya daga cikin wadannan budin ya rasa karafunansa. Yaji wani ihun, ya haura zuwaga dan belen, yayi kallo.
Bugun zuciyarsa ya karu. Ararrabe a cikin babban, kewayayyen wurin horon yaga dozin dozin na sabobbin dauka----har da yan’uwansa. Sun yi sahu, duk sun fuskanci yan Silver guda goma sha biyu. Mayakan sarkin suna tafiya a cikinsu, suna auna su da idanu.
Wata kungiyan sabobbin daukan kuma na saye daga gefe, karkashin kulawan wani mayaki, suna wurga mashoshi ga wani abun aunawa da nisa. Waninsu bai samu ma’aunin ba.
Hanyoyin jinin Thor sun kumbura da haushi. Shi zai iya harbin wadannan abin aunawan; shi gwanine Kaman kowanne daga cikinsu. Kawai domin sun girmeshi, kuma shi ya dan fisu kankanta, ba a yi adalci ba da a ka barshi a ka ki daukansa.
Basanmani, Thor yaji wata hanu a bayansa a yayinda hanun ta finciko shi zuwa ta baya ta kuma aika dashi a cikin iska. Ya fado da karfi a kasa, tare da rasa numfashi.
Ya kalli sama yaga mayakin bakin mashigin dazun, yana harararsa.
“Me na gaya maka, yaro?”
Kafin ya mayar da martini, mayakin yaja da baya ya harbi Thor da kafa kuma da karfi. Thor yaji wani hadadden kara a hakarkarinsa, a yayinda mayakin ke shirin sake bugashi.
Wannan lokacin, Thor ya kamo kafan mayakin a iska; ya finciko kafan, ya bata sayuwanshi sai yasa ya fado.
Thor ya taso zuwa kan kafafuwansa da sauri. A lokaci daya kuma, mayakin ma yatashi. Thor ya kalleshi, yana tsoron abinda shi ya aikata yanzu yanzu. A daya bangarensa, mayakin na huci da haushi.
“Ba kawai zan saka a turu ne kadai ba,” mayakin yace da rufafen baki, “har ma zan saka ka biya abinda kayi. Bawanda ya isa ya taba maitsaron fadan sarki! Ka manta da shiga runduna---yanzu zaka ruba a kurkuku! Zai zama babban sa’a in har an sake ganinka!”
Mayakin ya ciro wata sarka mai turu a karshen. Ya nufi Thor, da ramuko a nune a fuskarsa.
TunaninThor ya fara gudu. Ba zai iya yadda a sa shi a turu ba---duk da haka baya son ya jiwa wani daga cikin masu tsaron sarki. Dole yayi tunanin wani abu---kuma da gaggawa.
Sai ya tuna majajjabarsa. Hazakansa ya rigayeshi a yayin da ya kamoshi, yasa dutse, ya auna, sai ya sake dutsen.
Dutsen ya tafi a iska sai ya bige turun daga hanun mayakin dake cikin mamaki har yanzu; ya kuma samu yasun mayakin. Mayakin ya ja da baya yana girgiza hanunsa, yana ihu saboda zafi, a yayin da turun suka zuba a kasa.
Mayakin, tare da yiwa Thor kallo irin na mutuwa, ya fitar da takwafinsa. Takwafin yafito da ainihin, karan karfe.
“Wancan ya kasance kuskurenka na karshe,” yayi mumunan barazana, sai ya taso.
Thor bashi da wani zabi; wannan mutumin yaki ya barshi. Yasa wata dutsen a majajjabarsa ya wurga. Yayi awu da gangan---baya son ya kashe mayakin, amma dole ya sayar dashi. Saboda haka maimakon ya auni zuciyarsa, ko hanci, ko ido, ko kai, Thor ya auna wuri daya da yasan zai sayar dashi, amma ba zai kasheshi ba.
Tsakanin kafafuwan mayakin.
Ya saki dutsen ya bi iska---ba da dukkanin karfinsa ba, amma daidai abinda zai ka da mutumin.
Harbin ya kasance yaje dai dai.
Mayakin ya fado, yana mai sake takwafinsa, a yayinda ya kama kwalatansa ya fadi a kasa ya dunkulu Kaman kwallo.
“Zaka ratayu saboda wannan!” ya fadi acikin zafin ciwo. “Mayaka! Mayaka!”
Thor ya daga kai yaga daga dan nesa dayawan masu tsaron gidan sarki sun nufe shi.